Saturday 31 January 2026 - 20:10
Majalisar Shugabannin Makarantun Addini (Hauzozi) na Kasar Indiya Sun nuna Goyon Bayansu ga Ayatullahil Uzma Khamenei

Hauza/ Majalisar shugabannin makarantun addini (Hauzozi) na kasar Indiya ta fitar da wata sanarwa inda ta bayyana cikakken goyon bayanta ga Ayatullahil Uzma Sayyid Ali Khamenei, Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci na Iran, sannan ta yi Allah wadai da kakkausar murya game da katsalandan din da Amurka ke yi a yankin.

A cewar rahoton Ofishin Yada Labaran Hauza, Majalisar shugabannin Hauzozin kasar Indiya ta fitar da sanarwar ne a hukumance, inda ta bayyana goyon bayanta na dukkan ɓangarori ga Jagora Ayatullahil Uzma Sayyid Ali Khamenei (Dz). Haka kuma, ta yi Allah wadai da matakan da Amurka ke dauka a yankin kwanan nan, tana mai bayyana hakan a matsayin abin da ke rura wutar fitina da kuma barazana ga zaman lafiyar yankin da ma duniya baki daya.

Ga cikakken bayanin sanarwar:

Allah Madaukakin Sarki ya ce: “Kada ku yi rauni, kuma kada ku yi bakin ciki, alhali ku ne mafi daukaka idan kun kasance muminai.” (Al-Imran: 139).

Majalisar shugabannin Hauzozi na kasar Indiya, bisa nauyin da ya rataya a wuyanta na addini, ilimi, da dan adamtaka, tana bayyana matukar damuwarta game da karuwar barazana da matsin lamba na soji da gwamnatin Amurka da kawayenta ke yi wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Wadannan matakai sun saba wa ka’idojin shari’ar kasa da kasa, kundin tsarin mulkin Majalisar Dinkin Duniya, da kuma dokar hana amfani da karfi, wanda hakan ke jefa zaman lafiyar duniya cikin hadari.

A mahangar fikihun Musulunci, hankali na siyasa, da dokokin kasa da kasa, kowace irin barazana ta soji, killace tsaro, musamman ma magana a fili ko a fake game da kisan Jagoran addini kuma babban abin koyi (Marja'i) na al'ummar Musulmi, babban laifi ne da ya saba wa doka kuma bayyanannen misali ne na ta'addancin kasa. Wannan ba wai kawai ya saba wa ikon kasa mai cin gashin kanta ba ne, har ma cin fuska ne ga daruruwan miliyoyin Musulmi a fadin duniya.

Majalisar shugabannin Hauzozin Indiya tana bayyana cikakken goyon bayanta da tsayuwa tare da Ayatullahil Uzma Sayyid Ali Khamenei. Tana kallon sa a matsayin alamar hikimar addini, jagoranci na gari, da tsayin daka na adalci wajen yakar mulkin kama-karya na duniya. Duk wani cin zarafi ko barazana gare shi, tamkar cin zarafin daukacin al'ummar Musulmi ne.

Wannan majalisa tana jaddada cewa "kariya ga kai" hakki ne na halal ga al'ummar Iran wajen tunkarar kowace irin barazana daga waje. Matakan soji na Amurka ba su da wata madogara ta doka kuma ana iya daukarsu a matsayin manyan laifuka na kasa da kasa.

Tarihi ya nuna cewa manufofin katsalandan, takunkumai ba bisa ka'ida ba, da matsin lamba na siyasa, ba sa taba kawo tsaro; maimakon haka, su ne asalin rikice-rikice da rashin tsaro a yankin Gabas Ta Tsakiya (Yammacin Asiya) da ma duniya.

Majalisar shugabannin Hauzozin Indiya tana kira ga dukkan hukumomin kasa da kasa, musamman Majalisar Dinkin Duniya da Kwamitin Tsaro, da su sauke nauyin da ya rataya a wuyansu, su daina yin shiru game da ta'addancin kasa, sannan su hana afkuwar wani babbar musiba ta dan adam a yankin.

Muna imani cewa hanya daya tilo ta fita daga wannan rudani ita ce tattaunawa bisa mutunta juna, bin doka, da kauce wa son rai na bangare daya. Hauzozi a ko da yaushe suna goyon bayan zaman lafiya na adalci, mutuncin dan adam, da yaki da zalunci, kuma ba za su taba yin shiru a kan hakan ba.

Daga karshe, muna girmama ambaton sunan Imam Khumaini (r.a), wanda ya koyar da darasin girma da juriya ga al'ummai, inda ya taba fada da karfin gwiwa cewa: "Amurka ba ta isa ta tsinana komai ba."

A yau ma, al'ummar Musulmi sun yi imanin cewa kowane irin farmaki ko wuce gona da iri zai kare ne da kunya da rashin nasara ga maharan. "Taimako daga Allah yake, kuma nasara tana kusa, saboda haka ka yi wa muminai bushara."
Wassalamu Ala Man Ittaba'al Huda
Majalisar Shugabannin Hauzozi na Kasar Indiya

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha